Rikici na Kara Tsanani Tsakanin Palastinawa Da Yahudawa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i22480-rikici_na_kara_tsanani_tsakanin_palastinawa_da_yahudawa
A yayin da magabatan Haramcecciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da hana Al'ummar Palastinu gudanar da Salla a Masallacin Aksa, ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin magabatan bangarorin biyu.
(last modified 2018-08-22T07:00:26+00:00 )
Jul 22, 2017 14:47 UTC
  • Rikici na Kara Tsanani Tsakanin Palastinawa Da Yahudawa

A yayin da magabatan Haramcecciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da hana Al'ummar Palastinu gudanar da Salla a Masallacin Aksa, ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin magabatan bangarorin biyu.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya sanar da katse duk wata hulda ko kuma tattaunawa da mahukuntan Isra’ila, sakamakon matakan da suka dauka na hana jama’a isa ga masallacin Quds domin gudanar da ibada, lamarin da ya yi sanadiyyar barkewar tarzoma har ma da samun asarar rayuka.

Abbas ya bayyana cewa dole ne Isra’ila ta janye daruruwan jami’an tsaron da ta jibge a zagayen masallacin, tare da bai wa jama’a damar isa domin gudanar da ibada.

A jiya juma’a, artabun da aka yi tsakanin falasdinawa da jami’an tsaron na Isra’ila, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane6, uku Falasdinawa da kuma wasu yahudawa uku.

A cewar Mustapha Bargusi Babban saktaren kungiyar farar hula na Al'umma, magabatan HKI sun rufe mashiga takwas na Masallacin Aksa, wanda hakan ke nuna cewa Yahudawan na kokarin gwada karfin Sojin su a wannan wuri mai alfarma, lamarin da Al'ummar Palastinu da ma musulmin Duniya baki daya ba za su amince da shi ba.