Bangladesh : An Yankewa Mayakan Islama 10 Hukuncin Kisa
Aug 20, 2017 06:45 UTC
A kasar Bangladesh an yankewa wasu mayaka dake ikirari da sunan Islama hukuncin kisa, saboda samunsu da laifin yunkurin hallaka fira ministar kasar Sheikh Hasina.
Mutanen su guda goma kotu ta yanke masu hukuncin ne saboda hannun da suke da shi wajen haka wani makeken bam, a kusa da inda fira ministar Hasina ke shirin gabatar da wani jawabi a lokacin wa'addin mulkinta na farko.
Babban mai shigar da kara na gwamnatin kasar Shamsul Haq Badol ya ce an dana bam din ne domin hallaka fira ministan kasar da kuma wasu jiga-jigan jam'iyyar ta ta Awami a waccen lokacin.
Bayanai sun ce bam din da aka dana ya kai nauyin kilo 76.