Siriya : Fararen Hula Na Cikin Tsaka Mai Wuya A Raqa
Sama da fararen hula arba'in ne ciki har da yara suka gamu da ajalinsu a ci gaba da hare-haren sama da kawancen da Amurka ke kaiwa a birnin Raqa na Siriya.
Bayanai sun nuna cewa kawacen dake yaki da kungiyar Da'esh ya kwato kashi 60% na biranen da ke hannun 'yan ta'addan, inda tuni ya yi wa yankin kawanya, saidai lamarin ya rusa da fararen hula na yankin a cewar kungiyoyi masu zamen kansu.
A jiya Litini fararen hula 42 ne da suka hada yara 19 da kuma mata 12 ne suka rasa rayukansu a unguwanni da dama da kungiyar ta Da'esh ke rike da a cewar hukumar OSDH.
Kafin hakan dama wasu fararen hula 27 sun gamu da ajalisu a ranar lahadi data gabata.
Alkaluma dai sun nuna cewa kawaven dake yaki da kungiyar 'yan ta'addan ta IS ya kai hare-hare 250 a cikin mako guda kacal.