Dalilan Mahimancin Tsarkake Garin Tal'afar Na Kasar Iraki
A yayin da aka cikin kwanaki hudu na fara kai farmakin tsarkake garin tal'afar na kasar Iraki, duk wani shiri da kungiyar ISIS tayi na kare garin daga faduwa ya ruguje.
A ranar 20 ga watan wata na Augusta da muke ciki ne dakarun kasar Iraki suka fara kai farmakin tsarkake garin Tal'afar na jihar Nainuwa, kuma ana iya bayyana dalilai guda uku game da mahimancin na tsarkake wannan gari daga kangin 'yan ta'addar ISIS.
Dalili na farko: shi ne mahimancin da garin yake da, tal'afar dai gari ne dake karkashin jihar Nainuwa ta arewa maso yammacin kasar Iraki, kwana guda kacal da faduwar garin Mausil, 'yan ta'addar ISIS suka mamaye garin a watan yunin shekarar 2014, bayan girman da garin tal'afar ke da shi, garin na a matsayin sukurwa ta sada kasashen Iraki, Siriya da turkiya.tsakanin kan iyakokin kasashen Turkiya da siriya, kilomita 60 ne kacal, ko baya ga hakan garin tal'afar na a tsakanin gariruwan sanjar na 'yan kabilar kurdawa da Mausil na mabiya mazhabar ahlul-sunna, sannan kungiyar ta ISIS ta mayar da garin a matsayin babbar cibiyarta na horas da mayakanta tare da basu makamai, domin haka ne suke kiran garin da karamin Mausil, idan muka yi la'akari da wannan yanayi na garin Tal'afar, cin nasarar tsarkake shi ba ga kasar Iraki kawai zai yi tasiri ba, har ma da kasar Siriya.
Dalili na biyu kuma shi ne, yawan al'ummar dake cikin wannan gari, duk da cewa kimanin mutane dubu 300 na al'ummar garin dake a matsayin rabin mutane garin sun yi hijira a yayin da kungiyar ISIS ta mamaye shi, to amma mafi yawan mazauna garin kurdawa ne mabiyar mazhabar shi'a, domin haka ne masu sharhi kan harakokin siyasar gabas ta tsakiya ke ganin cewa mahimancin siyasa ya fi mahimancin da yanayin da garin ke da shi, saboda garin tal'afar wata mashiga ce ta shiga wasan siyasa ga mabiyar mazhabar shi'a da 'yan sunna.
Dalili na uku kuma shi ne, sabanin da aka fuskanta na shigar Dakarun sa kai na Hashadu-Sha'abi cikin ayyukan tsarkake garin na tal'afar, kamar yadda masu adawa da shiri, suka nuna adawar su a ayyukan tsarkake birnin Mausil tare da bayyana dalilin bangaranci na cewa mazauna garin Mausil din mabiyar mazhabar sunna ne, a wannan karo ma masu adawa da shirin, musaman ma kasar Turkiya na ganin cewa mazauna wannan gari,turkawa ne domin haka , bai kamata ma dakarun sa kai din na hashadu-sha'abi su shiga cikin wannan yaki, duk da wannan adawa, kamar yadda dakarun sa kai na hashadu-sha'abi suka taka mahimayar rawa wajen 'yanto garin Mausil, mai magana da dakarun hashadu-sha'abin ya bayyana cewa akwai mayaka dubu 25 dake ciki shiri na shiga cikin aikin 'yanto garin na Tal'afar.
Ganin wannan nasara da aka samu cikin kwanaki hudu da fara ayyukan tsarkake garin na tal'afar, masu sharhi kan harakokin tsaro na ganin cewa tsarkake garin daga hanun 'yan ta'addar ISIS ba zai fice makunni shida ba.