A Yau Ne Mahajjata Suke Gudanar Da Jifar Shaidan Jamratul Aqbah
Sep 01, 2017 06:48 UTC
Tun da jijjifin safiyar yau ne mahajjata kimanin miliyan biyu suka fara gudanar da jifar shaidan a ranar idin layya.
Rahotanni sun ce tun da jijjifin safiyar yau ne mahajjatan suka fara isa wurin jifar jamratul Aqbah, inda kimanin mahajjata miliyan biyu ne suke gudanar da wannan aikin ibda a bana.
Mahukuntan kasar saudiyya sun ce sun dauki dukkanin matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro da kuma tsaria yayin gudanar da jifan Shaidan.
Inda bayanin ya ce an saka na'urorin daukar hoto guda 500 a wurin, domin duba yadda komai yake gudana a wurin, da nufin ganin an kauce wa matsalar da aka samu ta tirmutsitsi a shekaru biyu da suka gabata, inda mutane fiye da dubu 7 suka rasa rayukansu.