Sojojin Siriya Sun Samu Babbar Nasara A Deir Ezzor
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i23759-sojojin_siriya_sun_samu_babbar_nasara_a_deir_ezzor
Sojojin kasar Siriya sun samu babbar nasara a yakin da suke da kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh a yankin Deir Ezzor dake gabashin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:39+00:00 )
Sep 05, 2017 09:54 UTC
  • Sojojin Siriya Sun Samu Babbar Nasara A Deir Ezzor

Sojojin kasar Siriya sun samu babbar nasara a yakin da suke da kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh a yankin Deir Ezzor dake gabashin kasar.

Kwace yankin Deir Ezzor da ya kunshi yankin dake da arzikin man fetur ya kwashe shekaru biyu karkashin ikon 'yan ta'addan.

Tuni shugaban kasar ta Siriya Bashar Al Assad ya jinjinawa dakarun kasar game da wannan babbar nasara.

Bayanai sun nuna cewa an samu nasara ce tare da taimakon dakarun Hizbollah da kuma sojojin kasar Rasha dake dafawa sojojin kasar ta Siriya.

Birnin da ya kunshi sama da mazauna dubu dari, ya rabu gida biyu ne tun a watan Yuli na 2014, kuma 'yan ta'addan na IS na rikeda kashi 60% na yankin dake da iyaka da kasar Iraki.