Tawagar Kurdawa Daga Arbil Ta Isa Birnin Bagadaza
Kurdawa Sun aike da tawaga zuwa Bagadaza kwanaki shida gabanin kuri'ar raba gardamar ballewa daga Iraki
Kafafen watsa labarun Iraki sun ce da safiyar yau talata ne tagawar Kurdawan daga Arbil ta isa birnin Bagadaza domin ganawa da mahukuntan kasar akan batun kuri'ar raba gardamar ballewa daga Iraki.
A gefe daya, shugaban kasar ta Iraki "Fu'ad Ma'asum" ya ce warware sabanin da ke tsakanin Bagadaza da Arbil shi ne muhimman batun da ke gabansu.
A ranar asabar din da ta gabata, Pira minista Haydar Abadi, ya yi barazanar amfani da karfin soja akan Kurdawan idan har suka nace sai sun balle daga Iraki.
A ranar 25 ga watan nan na Satumba ne dai Kurdawan suka tsaida za su yi kuri'ar raba gardama ta ballewa daga Iraki.