Jiragen Saman Yakin Saudiyya Sun Kashe Fararen Hula A Kasar Yamen
Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun kai wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan yankin garin Kasr da ke lardin Hajjah a shiyar arewa maso yammacin kasar Yamen.
Rahotonni daga Yamen suna bayyana cewa: Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun kai wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan yankin garin Kasr a yammacin yau Talata, inda suka kashe mutane 9 iyalan gida guda da suka hada da mata 4 da kananan yara 5.
Har ila yau jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun yi luguden wuta kan garin Asilan da ke lardin Shabwah a shiyar kudu maso gabashin kasar Yamen, amma ya zuwa yanzu babu irin hasarar da hare-haren suka janyo.
Tun a watan Maris na shekara ta 2015 jiragen saman yakin masarautar Saudiyya tare da cikekken goyon bayan kasar Amurka suka fara luguden wuta kan kasar Yamen bisa da'awar neman dawo da tsohon shugaban kasar mai murabus Abdu-Rabbuh Mansur Hadi kan karagar mulki domin samun damar ci gaba da aiwatar da munanan manufofinsu kan kasar ta Yamen.