Bom Kirar Amurka Ne Ya Kashe Yara A Yemen_ Amnesty
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i24261-bom_kirar_amurka_ne_ya_kashe_yara_a_yemen_amnesty
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa cewa da Amnesty International, ta fitar da wani rahoto yau Juma'a dake cewa wani bom kirar Amurka ne akayi amfani da shi wajen kai hari a wani gida dake birnin Sanaa na kasar Yemen, inda rayukan mutane da dama galibi yara suka salwanta.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Sep 22, 2017 11:37 UTC
  • Bom Kirar Amurka Ne Ya Kashe Yara A Yemen_ Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa cewa da Amnesty International, ta fitar da wani rahoto yau Juma'a dake cewa wani bom kirar Amurka ne akayi amfani da shi wajen kai hari a wani gida dake birnin Sanaa na kasar Yemen, inda rayukan mutane da dama galibi yara suka salwanta.

Rahoton ya ce harin sama da kawancen kasa da kasa da Saudiya ke jagoranta ya kai a ranar 25 ga watan Agustan da ya gabata a wasu gidaje biyu dake anguwar Faj Attan ya yi kashe mutane 16 ciki har da yara 7.

Babbar Darektar kungiyar ta Amnesty a yankin gabas ta tsakiya, Lynn Maalouf, ta fada a cikin rahoton cewa bayan kaddamar da bincike kan guntsiran bom din a yanzu mun tabbatar da cewa kirar Amurka ne.

Harin dai ya yi sanadin mutuwar iyalan yarinya nan da ake ce ma Buthaina wacce kafofin yada labarai suka yi yayata hotinan ta bayan harin, wanda ya yi ajalin iyayenta da kanninta maza da mata da kuma wasu fararen hula.

Bayan lamarin dai, kawancen da Saudiyya ke jagoranta a amsa cewa shi ya kai harin, amman a cewarsa bisa kuskure ne.

Saudiyya dai babbar abokiyyar cinikin kayan yaki ce ga kasashen yamma musamen ga Amurka. 

Tun dai bayan da Saudiyya ta kaddamar da kai harin ba gairi ba dalili a wannan kasa ta Yemen, alkalumen da MDD ta fitar sun nuna cewa sama da mutane 8,500 suka rasa rayukansu da suka hada da yara 1,700.