Sojojin Iraki Sun Sauke Tutar Kurdawa Da Kudancin Karkuk
Oct 14, 2017 08:19 UTC
Bayan da sojojin na Iraki suka sauke tutar ta Kurdawa sun maye gurbinta da ta Iraki.
Sojojin na Iraki sun fara taruwa a kusa da birnin Karkuk da ake da sabani akansa, tsakanin gwamnatin tsakiya da kuma ta yankin Kurdawa.
Majiyar tsaron kasar ta Iraki ta ce, matakin aikewa da sojojin shi ne shimfida ikon Bagadaza akan yankunan da ake da sabani akansu.
Kwamandan dakarun sa kai na "Hashd-sha'abi' Hadi al-amuri' ya yi kira ga mayakan kurdawa, na "Pesh-margah' da su fice daga yankunan da suke iko da su.
A baya, Mas'ud Barzani ya aike da mayakan Peshmarga zuwa yankin domin su kare yankin.