Dakarun Ali Khalifa Sun Killace Gidan ayatollahi Isa Kasim
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i25289-dakarun_ali_khalifa_sun_killace_gidan_ayatollahi_isa_kasim
Dakarun Yaki da tawayen na kasar Bahren sun kai farmaki gidan jagoran mabiya mazhabar shi'a na kasar ayatollahi Isa Kasim tare da killace shi.
(last modified 2018-08-22T07:00:56+00:00 )
Nov 02, 2017 14:48 UTC
  • Dakarun Ali Khalifa Sun Killace Gidan ayatollahi Isa Kasim

Dakarun Yaki da tawayen na kasar Bahren sun kai farmaki gidan jagoran mabiya mazhabar shi'a na kasar ayatollahi Isa Kasim tare da killace shi.

Tashar telbijin Al-alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin tehran ta habarta cewa a wannan alkhamis dakarun kasar Bahren masu yaki da tawaye cikin manyan motoci yaki da masu sulke sun kai sumame yankin adderaz kusa da gidan ayatollahi isa kasim jagoran mabiya mazhabar shi'a.

A ranar 21 ga watan Mayun 2017 ne kotun a kasar ta Bahren ta yanke hukuncin daurin talala na shekara guda bisa zargin ingaza mutane a kan neman hakinsu tare da tarar dinari dubu 100 kwatamkacin dalar Amurka dubu 265.

Baya ga hakan kotun ta yankin hukuncin daurin shekara guda a gidan yari ga wani babban malami mai suna muhyidin Almash'al bisa tuhumarsa da goyon bayan masu zanga-zanga na neman hakinsu a kasar, har ila yau kotun ta yanke hukuncin daurin watani shida a gidan yari ga wasu maliman guda biyu da suka hada da Shekh  Adil Asha'ala da shekh Hani Albaraza tare da yi musu tara da kudi.

A ranar larabar da ta gabata ce al'ummar kasar Bahren a yankuna daban daban na kasar suka gudanar da zanga-zangar goyon bayan ayatollah shekh isa kasim da sauran maliman da gwamnati ta kame.