Nabeeh Berri:Murabus Din Hariri Ya Saba Doka
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i25380-nabeeh_berri_murabus_din_hariri_ya_saba_doka
Shugaban Majalisar dokokin kasar Labnon ya ce murabus din da Piraministan kasar Sa'ad Hariri yayi, ya sabawa doka kuma ba za a amince da shi ba.
(last modified 2018-08-22T07:00:57+00:00 )
Nov 08, 2017 14:42 UTC
  • Nabeeh Berri:Murabus Din Hariri Ya Saba Doka

Shugaban Majalisar dokokin kasar Labnon ya ce murabus din da Piraministan kasar Sa'ad Hariri yayi, ya sabawa doka kuma ba za a amince da shi ba.

Kafar watsa labaran kasar Labnon ta nakalto Nabeeh Berri shugaban malajisar dokokin kasar Labnon a wannan laraba na cewa murabus din da Piraministan kasar Sa'ad Hairi ya yi sabawa kundin tsarin milkin kasar domin haka ya zama wajibi ya dawo kasarsa sannan ya gabatar da bukatarsa ga shugaban kasar kamar yadda doka ta tsara.

Nabeeh Berri ya ce gwamnatin kasar Labnon za ta kasance cikin karfinta kuma wannan murabusa na sa'ad Hariri bai zai canza wani abu game da yanayin kasar ba.

Shugaban majalisar dokokin kasar Labnon ya kara da cewa za a amince da murabus din da tayi daidai da dokokin kasar ne domin haka gwamnati ba ta dauki ko wani irin kudiri ba bayan da ta saurari bayyanan yin murabus din Piraminista Sa'ad Hariri

A ranar Assabar din da ta gabata ce Piraministan na kasar Labnon Sa'ad hariri ya sanar da murabus dinsa daga birnin Riyyad na kasar Saudiya