Matsin Lambar Bayan Fage Na Fitar Iran Daga Siriya
Duk da cewa kasar Iran, kasa ce da ta tsayin daka wajen fada da kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar Siriya, to sai dai a yayin da ake gaf da kawo karshen 'yan ta'addar, masu goyon bayan su na kokarin fitar da kasar Iran din ta bayan fage daga kasar Siriya, domin share fage na sake dawo da 'yan ta'addar a yankin.
A kokari da magoya bayan 'yan ta'addar ke yi na kawar da gwagwarmaya a yankin gabas ta tsakiya tare da sake dawo da 'yan ta'adda a yankin, sakataren harakokin wajen Amurka Rex W. Tillerson ya ce wajibi ne dakarun kasar Iran da suka hada da dakarun juyin juya halin musulinci da kuma dakarun da suke samun goyon bayansu su bar kasar Siriya su koma kasashen su.
A matsayin mayar da martani, Ministan harakokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya ce shigar dakarun kasar Iran Siriya yana bisa doka, kuma jita-jitar da ake watsawa na sanya lokacin fitar dakarun Rasha daga kasar siriya ba gaskiya ba ne, tattaunawar da kasashen Iran, Rasha da Turkiya ke ci gaba da yi kan kasar Siriya ya taimaka wajen dawo da tsaro a kasar, mai yiyuwa da ba a gudanar da wannan tattaunawa ba, da yanzu kungiyar ta'addancin IS ba tayi rauni kamar yadda take a yanzu ba.
Wannan tattaunawa da ake yi ba tare da kasashen yamma ba, shi ne ya sanya suke kokarin yin matsin lamba ga MDD ta sanya Dakarun gwagwarmaya kamar na kungiyar Hizbullah da masu kare hubbarorin iyalan gidan manzon Allah tsarkaka fita daga cikin kasar Siriya, da hakan zai basu dama su sake shirya wasu 'yan ta'addar a kasar.
A nata bangare jamhuriyar musulinci ta Iran ta sha nanata cewa kasancewar dakarunta masu kare harami,da kwararu masu bayar da shawara a fagen yaki na zuwa ne bisa bukatar gwamnatin Siriya da kuma taimakon al'ummar kasar domin yaki da 'yan ta'adda. Da dai kasar Iran din ta tura dakarunta bisa bukatar Rasha ko Amurka, to da sai tayi jiran izini daga wadannan kasashe na fitar da dakarunta daga kasar ta Siriya,amma lokaci da kasa mai 'yanci kamar Iran ta amsa bukatar zababbiyar gwamnati da bukatar al'ummar yankin, wajen taimako na bayar da kariya, ba za ta iya jiran izinin wata kasa ba domin kawo karshen wannan taimako.
A cikin 'yan kwanakin nan babu wata magana da kasashen yamma da saudiya ke yi face fitar Iran daga kasar Siriya bisa dalilan kawo karshen kungiyar IS a kasar, to sai dai abin tambaya a nan me nene dalilin da ya sanya su wadannan kasashe ba sa janye sansanonin sojojinsu daga yankin? misali me nene ya sanya Amurka ta ki janye dakarunta daga kasar Afganistan bayan kawo karshen gwamnatin taliban? sai dai ma kara yawan sojojinta tayi a cikin kasar.
A fili yake, wannan kokarin da kasashen yamma tare da wasu kasashen yankin ke yi na kawo karshen zaman dakarun Iran a Siriya, sakamakon tsoron da suke da shi na cewa kasar Iran za ta samu wuri a zukatan al'ummar yankin da duniyar musulinci, kamar yadda hakan ta kasance a kasashen Iraki da Yemen har ma suka kafa rundunar sa kai wajen yakar zalinci ta yadda wadannan kasashe suka kasa cin nasara wajen jefa yanayin tsaron yankin cikin hadari.