Kungiyar (EU) da Turkiyya sun cimma matsaya kan kwararar bakin haure
Mar 17, 2016 05:30 UTC
kungiyar tarrayya turai da Turkiyya sun cimma matsaya guda akan bakin haure dake kwararar teku domin shiga Turai ba bisa ka'ida ba.
kasashen 28 membobin kungiyar da Turkiyya sun cimma wannan matsaya ne domin gane ma juna akan yadda za'a magance matsalar bakin hauren dake kwarara turai ba bisa ka'ida ba.
kazalika yerjejeniyar ta tanadi dage halascin shiga turai ga 'yan Turkiyya sai da takardar visa kafin karshen watan Yuni shekaran nan, da gaggauta shirin shigar da wannan kasa memba a kungiyar ta Eu, tare da kwashe 'yan gudun hijira Syria sama da 72,000 dake sansanin 'yan gudun hijira Turkiyya zuwa Turai da taimakon hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD.