Yemen: An Kashe Sojojin Saudiyya Da Dama A Yankin Jizan
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i25899-yemen_an_kashe_sojojin_saudiyya_da_dama_a_yankin_jizan
Sojojin kasar Yamen da suke maida martani akan wuce gonar Saudiyya, sun kai hari a gundumar Jizan na Saudiyya tare da kashe sojojin wannan kasa masu yawa.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Nov 30, 2017 08:26 UTC
  • Yemen: An Kashe Sojojin Saudiyya Da Dama A Yankin Jizan

Sojojin kasar Yamen da suke maida martani akan wuce gonar Saudiyya, sun kai hari a gundumar Jizan na Saudiyya tare da kashe sojojin wannan kasa masu yawa.

Majiyar tsaron kasar Yemen ta shaidawa tashar telbijin din al'alam cewa; Sun ka hare-haren ne a yankunan al-hamraa da kuma alkumamah, tare da kashe sojojin Saudiyya da dama.

Sojojin na Yemen sun yi amfani da manyan bindigogi wajen kai harin akan sojojin Saudiyyar da kuma 'yan korensu da suke akan mashigar al-Dhawal.

Bugu da kari, dakarun sa kai na kasar Yemen din sun kai wani harin a yankin Khasbah a Jizan.

Sojojin na Yemen suna kai hari ne dai domin maida martani akan hare-hare da Saudiyya take kai wa kasarsu na tsawon shekaru uku a jere.