Hizbullah Ta Lebanon Ta Jininawa 'Yan Majalisar Kasar Tunisiya
'Yan Majalisar kungiyar ta Hizbullah sun yabawa kin amincewar 'yan majalisar kasar Tunisiya da bayyana jingawa Hizbullah ta'addanci da Kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta yi.
Da safiyar yau asabar ne shugaban kwamitin wakilan Hizbullah a Majalisar kasar Lebanon, Muhammad Ra'ad, ya aikewa da takwarorinsa na Tunisiya wasika da aciki ya bayyana takaicinsa da cewa; Wadanda suka jinginawa Hizbullah karairayi, su ne wadanda ya kamata ace suna taimakawa gwagwarmatar fada da masu mamayar Palasdinu.
Muhammad Ra'ad ya kuma ce; Kokarin bata sunan gwgawarmaya ya biyo bayan nasarar da suka samu ne akan 'yan Sahayoniya.
'Yan Majalisar kasar Tunisiya 41 ne suka fitar da bayani da a cikin suka yi tir da bayanin bayan taron kasashen larabawa akan kungiyar ta Hizbullah.