Syria: Harin Makamin Roka A Birnin Damascuss Ya Kashe Mutane Biyu
Dec 04, 2017 15:24 UTC
Majiyar tsaro a kasar Syria ta ce 'yan tawaye sun harba makamin roka ne akan yankin Abbasiyyin da ke cikin babban birnin kasar tare da kashe mutane biyu dakuma jikkata wasu bakwai.
Majiyar ta ci gaba da cewa; Yan tawayen sun kuma harba wasu makaman akan yankin Jarmanah da ke kusa da birnin Damascuss, tare da haddasa barna mai yawa.
Wani labarin ya ce; kauyuka da garuruwa 28 da ke a kudanci da gabacin gundumar Hamas, sun koma karkashin ikon gwamnati daga hannun masu makamai, kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wuta ta tanada.
Tun a 2011 ne kasar Syria ta fada cikin yaki da hare-haren ta'addanci daga kungiyoyin da Saudiyya da Amurka su ke goyawa baya.