EU Ta Cimma Matsaya Kan 'Yan Gudun Hijira
Mar 18, 2016 06:36 UTC
Shugabannin kasashen 28 na kungiyyar tarayya Turai sun cimma matsaya wadda za a gabatar wa Turkyiya domin kai ga cimma yarjejeniyar magance matsalar kwararar ‘yan gudun hijira.
Firaminsitan Luxembourg, Xavier Bettel ya ce, a safiyar yau jumma’a za a gabatar da matsayar ga Firaministan Turkiyya Ahmet Davutoglu .
Matsayar dai za ta bukaci a maido da ‘yan gudun hijirar da ke kaura daga Turkiya zuwa Girka yayin da ake tsammanin kungiyar ta EU za ta bai wa Turkiyyan tallafin kudade tare da sanya ta cikin jerin kasashe memba a harkokin zirga zirga tsakanin ta da tarayyar Turai.