Yemen: Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kashe Fararen Hula Da Dama
Majiyar tsaron kasar Yemen ta ce a kalla mutane 23 ne suka kwanta dama sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin na Saudiyya suka kai wa kasar a jiya asabar.
Majiyar ta ci gaba da cewa; Jiragen yakin na Saudiyya sun kai hari ne a yankin Sha'aban, da garin Razih da suke a gundunar Sa'adah, wanda ya ci rayukan mutane 15.
Bugu da kari, jiragen yakin na Saudiyya sun kai wasu hare-haren a yankin "Bani Mu'az' da ke garin Sahhar a garin Sa'adha wanda ya dauki rayukan fararen hula 8.
A yankunan 'Dhibatul-Ismi' da 'Fara'a' da ke garin Kataf, jiragen yakin na Saudiyya sun kai hare-hare har sau uku daya, bayan daya.
Kasar Saudiyya wacce take samun goyon bayan Amurka ta bude yaki akan Yemen tun a cikin watan Maris 2015, wanda kuma zuwa yanzu ya ci rayukan mutane fiye da 12,000 bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya