Trump, Qudus Da Dokokin Kasa Da Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i26223-trump_qudus_da_dokokin_kasa_da_kasa
Bincike ya tabbatar da cewa matakin da Shugaban Amurka ya dauka na ayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin HKI ya yi hanun riga da dokokin kasa da kasa.
(last modified 2018-08-22T07:01:07+00:00 )
Dec 10, 2017 23:43 UTC
  • Trump, Qudus Da Dokokin Kasa Da Kasa

Bincike ya tabbatar da cewa matakin da Shugaban Amurka ya dauka na ayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin HKI ya yi hanun riga da dokokin kasa da kasa.

Ana iya bayyana matakin da Trump ya dauka a matsayin matakin da karya dokokin kasa da kasa a zahiri, da kuma tsarin Amurka na hukunci a kan tsarin duniya, a hakikanin gaskiya, kasar Amurka na taka muhimiyar rawa a tsarin da duniya ke tafiya kansa a halin yanzu, to amma shugaban kasar na yanzu, ya sa kafa ya ture wannan tsari, tare kuma da bayyana rashin amincewarsa da shi, a game da hakan, jaridar Le Monde ta kasar Faransa ta rubuta cewa matakin da shugaba Trump ya dauka a game da birnin Qudus  bai samu amincewar kawayen Amurka ba, kuma irin wannan mataki shi ne ya janyo yakin duniya na biyu.

A bangare guda kuma wannan mataki na shugaba Trump ya sabawa dokokin da kasashen duniya suka dauke game da birnin na Qudus, daga cikin su dokar kwamitin tsaro na MDD bayan yakin shekarar 1967, kwamitin tsaron MDD ya samar da doka mai lamba 242, da ta bayyana cewa wuraren da HKI ta mamaye da suka hada da tudun Golan na kasar Siriya, Zirin Gaza, Gabar tekun Jodan, ba sa daga cikin yankin Isra'ila, kuma dole ne hukumomin Isra'ila su janye daga wadannan yankuna.a halin da ake ciki, ba wai HKI ta janye daga wadannan yankuna ba kawai, a'a har ma ga shi yau shugaban Amurka ya bayar da kautar Qudus ga hukumomin HKI, wanda kuma hakan ya sabawa wannan doka.a cikin shekarun baya bayan nan Kwamitin tsaron MDD ya samar da dokar cewa bangaren gabashin Qudus na al'ummar Palastinu ne, a cikin watan Nuwambar 2015 MDD ta samar da dokoki guda shida kan HKI, daga cikin su kasashen duniya sun bayyana rashin amincewarsu da gine gine da hukumomin HKI ke yi a yankunan Palastinawa da kuma hana su kai kawo a Baitul-Makdis da kuma kokarin canza wani bangare nasa tare  da bayyana shi a matsayin abinda ya sabawa doka da kuma ba za a laminta da shi ba.

Matakin Shugaba Trump na Amurka ya sabawa doka mai lamba 2231 na kwamitin tsaron MDD wacce aka samar a watan Decembar 2016 wacce tayi alawadai da sabin gine gine da Isra'ila ke yi a mazugunin yahudawa 'yan kama wuri zauna, wannan mataki na shugaba Trump ba wai kawai bayar da izini ne ga mahukuntan Isra'ila na ci gaba da gine-ginen kamar yadda gwamnatin ta HKI ta dauki kudirin gina gidaje dubu 14 jim kadan bayan sanarwar ta Trump, saidai wannan ya nuna cewa gine gine a yankunan Palastinawan na bisa kan doka a mahangar Amurka.

Jaridar ta Le Monde ta ce jawabin na Trump ya bayyana Qudus babban birnin HKI a matsayin wata gaskiya, to saidai bai ishara a kan Qudus ta gabas ba a matsayin babban birnin Palastinu, wanda hakan kuma ya sabawa dokokin da duniya ta amince da shi,  wannan kuma shike nuna cewa kiyaye hakkokin kasa da kasa ba shi da wuri a siyasar harakokin wajen Trump.