Yeman : MDD Ta Zargi Saudiyya Da Kai Farmaki Kan Fararen Hula
Mar 19, 2016 07:20 UTC
MDD ta nuna damuwa matuka dangane da yadda Saudiyya ke ci gaba da kai farmaki kan fararen hula a kasar Yemen.
kazalika MDD ta yi allawadai da yadda farmakin da kawacen da Saudiyya ke jagoranta ke shafar fararen hula wadanda basu ji basu gani ba, kamar yadda babban kwamishinan hukumar kare hakin bil adama ta MDD Zaeid Raad al-Hussain ya sanar.
wannann dai na zuwa bayan kazamin farmakin da Saudiyya ta kai ranar Talata data gabata a kasuwa Al-Khamees dake arewa maso yammacin kasar ta Yemen, inda fararen hula 106 galibi yara kanana suka rasa rayukan su.