Hezbollah Za Ta Ci Gaba Da Yakar 'Yan Ta'ada A Syria
Mar 19, 2016 07:20 UTC
kungiyar Hezbollah ta Labonan ta ce ba gudu ba ja da baya game da yakin da take da kungiyoyin 'yan ta'ada a Syria.
Da yake bayyana hakan mukadashin sakatare janar na kungiyar Sheikh Naim Qasim, ya ce janyewar sojojin Rasha a Syria ba shi da wata alaka da yakin da suke da kungiyoyin 'yan ta'ada masu kafirta muslmai irin su da Da'esh da Al'Nosra.
ya kara da cewa sojojin Syria da dakarun Hezbolla nada karfin da zasu ci gaba da yaki da 'yan ta'adan a wannan kasa.