Birnin Kudus Na Musulmi Ne Har Abada.
To a yau za mu kawo mu ku batun da ya mamaye kafafen watsa labaru ne a cikin kwanakin nan. Wato batun birnin Kudus, da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bai wa haramtacciyar Kasar Isra'ila don ya zam ababban birninta.
Matakin da gwamnatin Amurkan ta dauka na yarda da birnin Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar Kasar Isra'ila, ya sake tabbatar da cewa ita, kasa ce wacce ba ta ganin kimar dokokin kasa da kasa balle ta girmama su. Abinda Trump ya yi, keta dokokin kasa da kasa ne, da kuma wulakanta dukkanin kasashen duniya, musamman kasashen musulmi da birnin na kudus yake wani bangare na tarihin addininsu.
Donald Trump ya dauki wannan matakin ne adaidai lokacin da haramtacciyar Kasar Isra'ila ta fada cikin tsaka mai wuya a siyasarta ta yanki. Don haka matakin da Shugaban na Amurka ya dauka ya zo ne a matsayin busa rai, ga haramtacciyar kasar, sannan kuma a lokaci guda da haddasa wani sabon rikici a cikin wannan yankin na gabas ta tsakiya.
Gwamnatocin Amurka da suka gabata sun yi kokarin mayar da ofishin jakadancin kasar zuwa birnin Kudus, amma sun dakata saboda la'akari da wasu abubuwa.
A wannan lokacin da Donald Trump ya bai wa Haramtacciyar kasar Isra'ila abinda bai mallaka ba, kasarsa da 'yan sahayoniya za su yi duk abinda za su iya domin kai wa ga manufarsu. Haddasa rikici da sabani a tsakanin kasashen musulmi yana daga cikin abinda za su sanya agaba. A cikin jawaban da Natanyaho ya rika gabatarwa a cikin kwanakin nan ya rika amabata jerin sunayen kasashen larabawan da su ke kulla akala da yan sahayoniyar a boye.
Abinda Amurkan ta yi, mataki ne mai hatsari da ya wajabtawa koda da kowa yunkurawa domin kare birni da masallacin Kudus. Domin kuwa gwargwadon yadda lokaci yake tafiya idan har ba a dauki matakin da ya dace ba a lokacin da ya dace, lamari zai zama jiki.
Da akwai dalilai masu yawa da suke nuni da cewa Amurkan tana son samar da sauye-sauye a cikin yankin gabas ta tsakiya. Dukkanin sauye-sauyen na Amurka suna da manufa guda da ita ce tabbatar da fifikon haramtacciyar kasar Isra'ila akan kasashen musulmi.
Saboda yadda wannan batun yake da girma da jefa wannan yankin cikin damuwa, hatta kasar Saudiyya wacce take da kawance kut da kut da Amurka, ta nuna kin amincewa na zahiri akan batun. Wani daga cikin jami'an Saudiyya ya bayyana cewa;
"Wannan matakin yana da sakamo mai hatsari, zai kuma bakantawa dukkanin musulmi."
Har ila yau, ya ci gaba da cewa: " Wannan matakin na Amurka ya nuna yadda ba za ta iya zama mai shiga tsakani ba akan batun Palasdinu. Daukar mataki akan makomar birnin Kudus, ya kamata a ce ya zo ne a mataki na karshe a tattaunawar Palasdinawa da Isra'ial."
Matakin na Trump zai rusa abinda ya saura da ake kira shirin zaman lafiya wanda Amurka take riya cewa tana shiga tsakani. Kuma fakewa da sunan taimakawa Palasdinawa wajen kulla alakar Saudiyya da haramtacciyar kasar Isra'ila, zai rasa duk wani dalili na gasmarwa.
Daukar Birnin Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar Kasar Isra'ila da Trump ya yi, zai kara bai wa Natanyaho karfin guiwar kara rashin ta ido.
A fili yake cewa al'ummar musulmi suna daukar matakin na Trump a matsayin hatsari mai girma ga wuraren masu tsarki kamar masalalcin Kudus. Kuma babu shakka musulmi biliyan daya da rabi da ake da su a duniya za su tunzura saboda wannan matakin.
Babu shakka akan cewa siyasa maras kan gado da Turmp yake bi, tana a matsayin babbar barazana ce ga tsaron wannan yankin na gabas ta tsakiya da kuma duniya baki daya.
Kungiyar 'yanto da Palasdinu wacce ta shahara da siyasa mai sassauci, ta yi gargadi da cewa:
" Daukar Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila yana nufin mutuwar tattaunawar sulhu da zaman lafiya."
Husam, Zumlut wanda shi ne shugaban ofishin kungiyar ta PLO a birnin Washington ya ce;
" Matakin da Amurkan ta dauka ya kashe tattaunawar sulhu."
Wannan irin mataki ma'anarsa ita ce samar da sauyi a cikin siyasar Amurka a gabas ta tsakiya. Kuma bude kafar rikice-rikice da tashin hankali a cikin yankin. Kuma a karshe, zai iya kawo karshen rawar siyasar Amurkan a cikin yankin.
Kamfanin dillancin labarum Reuters ya nakalto cewa Amurkan ta bukaci Isra'ila da ta kaucewa maida martani akan rikice-rikicen da za su iya faruwa, domin za su cutar da manufofin Amurka a cikin yankin.
Wani sashe na kiran Amurkan ga haramtacciyar kasar Isra'ila ya kunshi cewa:
"Tare da cewa mun san za ku yi farin ciki da wannan matakin na daukar Kudus a matsayin babban birni, sai dai muna kiran ku da kuma maida martani wanda ya dace akan rashin yarda da za a nuna."
Za mu dauki matakan da suka dace a cikin gabas ta tsakiya da kuma duniya domin fuskantar abinda zai faru, sannan kuma za mu yi nazarin abinda ya faru, da daukar mataki a cikin cibiyoyinmu na soja da suke wajen Amurka."