Birnin Kudus Na Musulmi Ne Har Abada 3
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i26511-birnin_kudus_na_musulmi_ne_har_abada_3
To har yau dai muna duake da wata fuska ne akan batun Kudus na Palasdinu.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Dec 20, 2017 01:22 UTC
  •                Birnin Kudus Na Musulmi Ne Har Abada 3

To har yau dai muna duake da wata fuska ne akan batun Kudus na Palasdinu.

                                      

Gwamnatocin Amurka da suka gabata, sun ki aiwatar da dokar majalisar kasar ta Congress akan birnin Kudus a matsayin babban birnin birnin haramtacciyar Kasar Isra'ila. Sai dai Donald Trump tun a yakin neman zabe ya yi alkawalin zai aiwatar da wannan manufar matukar ya ci zabe, kuma abinda ya faru Kenan.

Kuma duk da cewa da akwai nuna kin amincwa a cikin wannan yankin na gabas ta tsakiya da kuma a duniya, shugaban na Amurka Donald Trump ya yi gaban kansa ya bayyana amincewa da zama birnin kudus a matsayin babban birnin kasar haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da yin alkawalin mayar da ofishin jakadancin Amurkan zuwa cikin birnin.

Wannan matakin da shugaban na Amurka ya dauka yana cin karo da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya. A cikin watan Decemba na 2016 Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da kuduri wanda ya kunshi cewa:

" Duk wani sauyi da zai faru akan iyakokin ranar 4 ga watan Yuni na 1967 daga ciki hadda birnin Kudus, ba za a yarda da shi ba , sai idan bangarorin da suke tattaunawa sun cimma matsaya ne akansa."

Yin dubu ga halattar Amurka, yana nuni da cewa kasantuwar ta babbar mai goyon bayan haramtacciyar kasar Isra'ila, akodayaushe tana kokarin karfafa wannan haramtacciyar kasar ne. Kuma domin cimma wannan manufa tana yin kutse a cikin harkokin siyasa, tattalin arziki da al'adu na kasashe.

Jagoran juyin musulunci na Iran wanda ya gana da mambobin kungiyar Ahlulbayti (a.s) ta duniya da kuma mambobin kungiyar Radiyo da telbijin na kasashen musulmi, ya yi ishara da rawar da Amurka take takawa a cikin muhimman abubuwa guda uku.

Ya bayyana cewa: " Siyasar samar da baraka da sabani a tsakanin kasashen wannan yanki, Yin kutse a cikin siyasa da tattalin arziki da al'adu a cikin kasashen musulmi. Da kuma siyasar haddasa sabani a tsakanin al'ummar musulmi."

A halin yanzu Amurkan ta sake fito da wata fitinar wacce ta shafi aiwatar da matsayarta akan birnin kudus.

Shakka babu, da akwai daliali masu yawa da suka taka rawa wajen shiga wannan halin na yanzu.

Nuna sauki da gaskata alkawullan karya na Amurka da haramtacciyar Kasar Isra'ila, da wasu kasashe suka yi akan batun palasdinu, sun taka rawa wajen isa wannan halin da ake ciki.

Shakka babu, daya daga cikin rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a gabas ta tsakiya shi ne batun Palasdinu da mamayar da haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin fiye da rabin karni.

Imam Khumaini ( r.a) wanda ya assasa jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda yake da cikakkiyar masaniya akan dabi'ar haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma Amurka, ya ayyana ranar juma'ar karshe ta kowace juma'ar watan Ramdhan a matsayin ranar Kudus da duniya. Ranar ce ta tunatar da al'ummar musulmi muhimmnacin da ranar Kudus take da shi da kuma kasantuwarta a karkashin mamaya.

A wani daga cikin jawaban da ya gabatar akan wannan batun, Imam Khumai (r.a) yana cewa:

"Ranar Kudus, ba ranar palasdinawa ba ce kadai. Rana ce wacce ya zama wajibi ga dukkanin kasashe masu takama da karfi, da su fahimci cewa ba za su iya ci gaba da mamayar kasashen musulmi ba.

Ranar kudus, rana ce da ya zama wajibi mu gargadi dukkanin kasashe masu takama da karfi akan cewa; Musulunci ba zai sake ci gaba da cewa a karkashin kulawar muggan mutanen da ku ke dasawa ba. Ranar kudus rana ce ta farfadowar musulunci.:

Ayatullha Sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da jami'an gwamnati a lokacin bikin mauludin manzon Allah da Imam Ja'afar Sadik ya yi  bayani akan wannan batu na haramtacciyar Kasar Isra'ila.

Jagoran ya ce: "Amurka da 'yan sahayoniya, da kuma kasashen da suke damfare da su, su ne fir'aunonin wannan lokacin a duniya. Ya kuma bayyana yadda su ke kokarin haddasa sabani a tsakanin al'ummar musulmi.  Kuma wasu daga cikin 'yan siyasar Amurka cikin sani ko rashin sani, sun bayyana cewa dole ne a samar da yaki a cikin yankin yammacin Asiya da kuma yaki, domin haramtacciyar kasar Isra'ila ta zama ita kadai ne cikin aminci. Kuma kasashen musulmi da za su kasance a cikin fada ba za su taba samun ci ga baba.

Batun Palasdinu shi ne mafi muhimmanci ga duniyar musulmi. Don haka jagoran juyin ya bayyana cewa wajibi ga dukkanin al'ummar musulmi da su yi kokari domin ganin sun yantar da al'ummar palasdinu.

Bugu da kari, jagoran juyin, ya ce; gajiyawa ce ta sa makiyan addinin musuluncin suka bayyana birnin kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Sai dai shakka babu duniyar musulmi za su yi tsayin daka  wajen fuskantar 'yan sahayoniya, kuma shakka bbau palasdinu za ta zama 'yantacciya.

                                         ***

Wani sashe na jawabin Jagoran juyin musuluncin ya maida hankali ne akan bayyana boyayyun manufofin 'yan sahayoniya da Amurka dangane da wannan yankin da suka kunshi mayar da batun palasdinu zama gefe.

Shekaru uku da suka gabata, jagoran juyin ya bayyana cewa daya daga cikin ayyukan da suka zama wajbi al'ummar musulmi su sanya a gaba shi ne bai wa batun palasdinu muhimmanci. Ya bayyana cewa:

" Kada ku bari batun palasdinu da masallacinsa mai tsarki su zama abubuwan da aka manta da su. Wannan shi ne abinda makiya su ke so. Suna son duniyar musulmi su mance da batun paladinu."

Wajibi ne ga dukkanin duniyar musulmi su sake daura damara wajen fuskantar makircin makiya. Batun palasdinu shi ne mai muhimmanci, batu ne na alkiblar musulmi ta farko."