Turkiyya : Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane 2 A Santambul
Mar 19, 2016 07:22 UTC
Rahotanni daga Turkiya na cewa mutane biyu ne suka rasa rayukan su kana wasu bakwai suka raunana a wani harin kunar bakin wake a wata cibiyar kasuwanci dake tsakiyar birnin Satambul.
Harin na wannan safiyar ya faru ne a gafen wata hanya dake kaiwa zuwa cibiyar kasuwanci ta Istiklal a wuraren turawa dake birnin kamar yadda kafofin yadda labarai da dama na Turkiyya suka rawaito.
wannan dai zuwa kwanaki kadan bayan harin bam din da yayi sanadin mutuwar mutane 103 a harabar wata tashar motoci dake Ankara, wanda wata kungiyar Kurdawa ta dauki alhakin kaiwa.