Yemen: An Kashe 'Yan Koren Saudiyya 25 A Gabacin San'aa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i26713-yemen_an_kashe_'yan_koren_saudiyya_25_a_gabacin_san'aa
Majiyar sojan kasar ta Yemen ce ta sanar da kai harin akan 'yan koren saudiyya a yankin Nahum da ke gabacin babban birnin kasar Sanaa
(last modified 2018-08-22T07:01:12+00:00 )
Dec 26, 2017 03:59 UTC
  • Yemen: An Kashe 'Yan Koren Saudiyya 25 A Gabacin San'aa

Majiyar sojan kasar ta Yemen ce ta sanar da kai harin akan 'yan koren saudiyya a yankin Nahum da ke gabacin babban birnin kasar Sanaa

A wani gefen, jiragen yakin Saudiyya sun kai hare-hare har sau 20 a garin al-Khunja da ke gundumar al-Hudaidah a gabacin kasar tare da kashe wasu manoma 6.

Garin Hudaidah mai nisan kilo mita 226 daga birnin San'aa,yana da tashar jirgin ruwa mai muhimmnaci wacce Saudiyyar ta kasa kwace iko da ita a cikin shekaru biyu na yaki.

Saudiyya ta kafa kawancen larabawa da ya kunshi Hadaddiyar Daular larabawa da kuma Sudan domin yakar kasar Yemen da al'ummarta.

Fiye da mutane 13,000 ne suka kwanta dama saboda hare-haren na  kawancen Saudiyya