Yemen: Sojoji Sun Kwace Garin al-Khoja Da ke Gundumar Hudaidah.
Dec 28, 2017 15:33 UTC
Sojojin kasar Yemen da kuma dakarun sa kai na Ansarullah, sun sanar da kwace garin ne a yau alhamis.
A yayin kwace garin daga hannun yan koren Saudiyya, sojojin na Yemen sun kuma lalata motocin yaki masu sulke da kuma wasu kayan yaki.
A gefe daya, yan koren na Saudiyya da jiragen yakin na Saudiyya suke yi wa rakiya sun sha kashi a hannun "Ansarullah' a korarin da suka yi na isa yankin al-qaeda.
Dakarun sa kai na Ansarullah sun lalata tankokin yaki da motoci masu sulke a arewacin Ta'iz.
Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa bisa goyon bayan Amurka suna yakar Yemen tun 2015 har zuwa yanzu. Dubban mutane ne suka rasa rayukansu sanadiyyar yakin.