Turkiyya : Baki yan kasashen waje suka Mutu A Harin Santambul
Mar 20, 2016 02:24 UTC
Rahotanni daga Turkiyya na cewa, baki yan kasashen waje 4 ne suka rasu cikin harin bom da aka kai a cibiyar birnin santambul jiya Asabar.
Harin kunar bakin waken da aka tayar a titin Istikal Caddesi dake birnin Istambul, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 5, ciki harda wanda ya kai harin, sannan wasu mutane 36 suka jikkata. Sakamakon bincike da hukumar dokokin birnin Istambul ta bayar, an ce, Yahudawa 3 da wani dan kasar Iran sun rasu a harin.
Fadar White House ta Amurka ta ce 'yan kasarta 2 sun mutu a harin. Kuma wadanda suka jikkata masu yawon shakatawa ne, da suka fito daga kasar Ireland, Hadaddiyar Daular Larabawa, Isra'ila, Jamus, Iran, da Iceland.