Taron Wasu Kasasken Larabawa Kan Birnin Qudus
A ranar Asabar din da ta gabata ce wasu kasashen larabawa 6 da suka hada da Saudiya, Hadaddiyar daular larabawa, Jodan, Maroco, Palastinu da Masar tare da halartar babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Ahmad Abu Gaid suka gudanar da taro kan birnin Qudus ba tare da cimma wata matsaya ba.
Bayan wata guda, da matakin da ya sabawa dokokin kasa da kasa da shugaba Trump na Amurka ya dauka na ayyana birnin Qudus a matsayin hedkwatar haramtacciyar kasar Isra'ila tare kuma da bayar da umarni da mayar da Ofishin jakadancin kasar sa zuwa birnin Qudus,amma har yanzu babu mataki da kasashen Larabawa suka dauka na kalubalantar wannan mataki, saboda matsayar hukumomin Saudiya game da Haramtacciyar kasar Isra'ila, domin a halin da ake ciki mahukuntan Saudiyya sun shiga tsaka mai wuya a game da alakar su da Isra'ila.
A yayin da kyamar Isra'ila ke kara karuwa a tsakanin al'ummar musulmi musaman ma a duniyar kasashen Larabawa, mahuntar saudiya na ganin cewa tsanantar rikici tsakanin al'ummar Palastinu da Isra'ila shi zai kawo cikas ga kokarin da take yi na kulla alaka ta zahiri da Isra'ila, dangane da hakan ne, hukumomin saudiyar suka dauki kudirin kira taron kasashen Larabawa a watan Maris mai zuwa, domin bayyana uzurinsu na kin daukar matakin da ya dace game da Amurka da kuma Isra'ila, duk kuwa da cewa a baya hukumomin na Saudiya sun bayyana adawarsu da kiran taron gaggauwa game da matakin da shugaban Trump ya dauka game da birnin Qudus.
Jaridar NRC Handelsblad ta kasar Jamus cikin wani sharhi da ta rubuta game da tsoron da hukumomin Saudiya suke da shi na raguwar kyakkyawar alakar da suke da ita da Isra'ila, ta ce aiki tare tsakanin saudiya da Isra'ila da ake yi a boye cikin wannan shekara ta 2018 na iya kasancewa ya fi na shekarun da suka gabata, to sai dai tsanantar jayayyar dake tsakanin Yahudawa da Palastinawa na iya kawo wa saudiya cikas wajen shelanta kulla alakarta da Isra'la.
Wannan matsaya ta Saudiya ta janyo cikas a duniyar kasashen Larabawa wajen daukan kwararen matakai na kalubalantar matakin da Shugaba Trump ya dauka na shelantar birnin Qudus a matsayin babban birnin HK Isra'ila, duk da cewa jaridar New York Times ta Amurka ta watsa rahoton cewa Kasar Masar ta amince da matakin na Trump game da birnin Qudus tare da maye gurbin Babban birnin Palastinu da Birnin Ramallah, to saidai martanin da kasar Masar ta mayar da wasu kasashen kasashen Larabawa shi ke nuna cewa suna bayar da cikakken goyon baya ga al'ummar Palastinu.