An Zargi Amurka Da Hannu A Tashe-tashen Hankula A Iran
Jan 09, 2018 15:43 UTC
Wani tsohon jami'in Baitulmalin Amurka, -Paul Craig Roberts ne ya tabbatar da cewa kasarsa tana da hannu a cikin tashe-tashen hankulan da suka faru a Iran a makwannin da suka gabata.
-Paul Craig Roberts ya rubuta a shafinsa na internet cewa; A wani jikon Washington ta sake bude rikici da al'ummar Iran.
-Paul Craig Roberts ya ci gaba da cewa; Tun bayan juyin musulunci na Iran Amurka take tsoma bakinta a harkokin cikin gidan Iran tare da yin barna.
Bayan abinda ya faru a Iran, din kasar Amurka ta kira yi taron gaggawa na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya akan Iran, sai dai zaman ya kare da mai da Amurkan saniyar ware.
Tags