Ganawar Sarkin Saudiyya Da Tawagar 'Yan Majalisar Dokokin Amurka
Mar 21, 2016 12:25 UTC
Sarkin masarautar Saudiyya ya gana da wata tawagar 'yan majalisar dokokin Amurka a yau Litinin a birnin Riyad, dangane da batutuwa da suka shafi halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya bayar da rahoton cewa, Sarki Salman ya gana da tawagar yan majalisar dokokin kasar Amurkan ne kan batutuwan da suka shafi rikicin kasasar Syria da kuma yakin da kasar Saudiyya take yi a kan kasar Yemen.
Baya ga haka kuma sun tattauna batun ziyarar da shugaban kasar Amurka Barack Obama zai kai kasar ta Saudiyya aranar 16 ga watan Afirilu mai kamawa, inda zai gana da sarkin na Saudiyya, da kuma sauran sarakunan kasashen larabawan yankin Tekun Fasha.