Siriya Ta Musunta Yin Amfani Da Makamai Masu Guda
Jan 24, 2018 07:41 UTC
Gwamnatin Siriya ta yi fatali da zargin da akewa dakarun kasar da amfani da makamai masu guba kan 'yan tawaye a kusa da birnin Damascos.
Haka zalika gwamnatin kasar ta kuma allawadai da zarge-zarge marar tushe da ake yi mata da amfanin da makamai masu guba.
A ranar Juma'a daga gabata ne kungiyar dake sa ido kan al'amuran kare hakkin bil adama a Siriya (OSDH) ta zargi dakarun gwamatin Siriya da amfani da makamai masu guba a yankin Ghouta da ke yammacin Damascos.
Siriya dai ta jima tana musunta zarge zargen da ake mata kan amfani da makamai masu guba, bayan da a cewar ta a 2013 ta amunce da bayyanawa da kuma mika makamanta masu guba bisa yarjejeniya da hukumar yaki da makamai masu guba.