An Harbo Jirgin Leken Asirin Saudiya A Yemen.
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i27589-an_harbo_jirgin_leken_asirin_saudiya_a_yemen.
Kungiyar Ansarullah ta kasar yemen ta sanar da harbo da wani jirgin leken asiri na kawancen saudiya a jahar Ma'arib na kasar.
(last modified 2018-08-22T07:01:20+00:00 )
Jan 25, 2018 02:55 UTC
  • An Harbo Jirgin Leken Asirin Saudiya A Yemen.

Kungiyar Ansarullah ta kasar yemen ta sanar da harbo da wani jirgin leken asiri na kawancen saudiya a jahar Ma'arib na kasar.

Tashar talabijin din Al'alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta nakalto tashar Talabijin din Almasira ta kasar Yemen na cewa a daren jiya Laraba, mayakan Ansarullah sun kakkabo wani jirgin leken asirin kawancen Saudiya a yankin Kharayeb Al Quramish a yammacin jahar Ma'arib dake tsakiyar kasar.

A ranar 30 ga watan Disamban shekarar da ta gabata ma, dakarun na kungiyar Ansarullah sun kakkabo irin wannan jirgi na leken asirin kawancen saudiya a kauyen Harad na jahar Hijjah dake yammacin kasar.

A bangare guda, mayakan sa kai na kasar sun kai farmaki kan wasu sansanoni na 'yan koren Saudiyya da ke dauke da makamai karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar da ya yi murabus Abdu Rabahu Mansoor Hadi tare da hallaka wani adadi daga cikin mabiyansa da kuma jikkata wasu da dama na daban.

A jiya Laraba ma Dakarun tsaron ta Yemen sun harba wasu makamai masu linzami a matattarar sojojin hayar saudiya a yanki na 9 dake cikin jahar Sana'a babban birnin kasar.

Tun a 2015 ne dai sojojin na kasar Saudiyya suka fara kai hari akan kasar Yemen tare da cikakken goyon bayan Amurka, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci fiye da rayuka 12,000 bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.