Yamaniwa 9 Suka Rasa Rayukansu Sanadiyar Harin Jiragen Yakin Saudiya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i27811-yamaniwa_9_suka_rasa_rayukansu_sanadiyar_harin_jiragen_yakin_saudiya
Jiragen yakin kawancen saudiya sun yi lugudar wuta a wani yanki na jahar Amran dake arewacin kasar Yemen, tare da jkashe mutane 7
(last modified 2018-08-22T07:01:22+00:00 )
Jan 31, 2018 14:44 UTC
  • Yamaniwa 9 Suka Rasa Rayukansu Sanadiyar Harin Jiragen Yakin Saudiya

Jiragen yakin kawancen saudiya sun yi lugudar wuta a wani yanki na jahar Amran dake arewacin kasar Yemen, tare da jkashe mutane 7

Kamfanin dillancin labaran Mehr ya nakalto tashar talabijin din Almasira ta kasar Yemen na cewa sakamakon ruwan bama-baman da jiragen yakin kawancen saudiya suka yi a gadar Al-ifrat dake jahar Amran, har ila yau wasu fararen hula da dama sun jikkata bayan da mutane 7 suka yi shahada.

A bangare guda, Dakarun tsaro tare da na sa kai sun mayar da martani kan harin wuce gona da iri na saudiya, inda suka kai hari a matattarar sojojin hayar saudiya dake yankin AL Mahashmah na gabashin jahar Ajauf dake arewacin kasar ta yemen tare da hallaka wani adadi mai yawa daga cikin su.

Har ila yau dakarun sa kai din na yemen sun tarwatsa wata mota dauke da sojojin hayar saudiya 23 da  makami mai lizzami  a yankin  AL Mahashma.

Tun a 2015 ne dai sojojin na kasar Saudiyya suka fara kai hari akan kasar Yemen tare da cikakken goyon bayan Amurka, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci fiye da rayuka 12,000 bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.