Kasar Yemen Ta Yi Watsi Da Kudurin Majalisar Dinkin Duniya
Majalisar Kasar Yemen ta fitar da bayani da a ciki ta ce; Kudurin da aka fitar yana nuni da cewa duniya ba ta shirya kawo karshen yakin da ake yi akan kasar ba.
Majalisar kasar ta Yemen ta ci gaba da cewa; Rahoton da ita kanta Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar akan yakin shekaru uku na zalunci akan kasar Yemen, ya tabbatar da cewa al'ummar kasar suna cikin wahala.
Har ila yau Majalisar ta kasar Yemen ta bukaci ganin an bude tattaunawa a tsakanin bangarori daban-daban na al'ummar kasar domin shimfida adalci a cikin kasar.
Gwamnatin ta Yemen mai alaka da Kungiyar Ansarullah ta nuna takaicinta akan kudurin Majalisar Dinkin Duniya da ya sake kakabawa kasar takunkumi.
Tun a 2015 ne dai Saudiyya da kawayenta suka shelanta yaki akan al'ummar Yemen wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci dubban rayuka.