Dakarun Sa Kai Na Iraki Sun Hade Da Dakarun Tsaron Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i28921-dakarun_sa_kai_na_iraki_sun_hade_da_dakarun_tsaron_kasar
Bisa umarinin Piraministan kasar Iraki, dakarun sa kai na kasar Hashadu-sha'abi sun hade da rundunar tsaron kasar.
(last modified 2018-08-22T07:01:32+00:00 )
Mar 09, 2018 08:15 UTC
  • Dakarun Sa Kai Na Iraki Sun Hade Da Dakarun Tsaron Kasar

Bisa umarinin Piraministan kasar Iraki, dakarun sa kai na kasar Hashadu-sha'abi sun hade da rundunar tsaron kasar.

A daren jiya alhamis, piraministan kasar Iraki, Haidar Abadi ya sanya hanu kan wani kudiri da ya bawa dakarun kai na hashadu sha'abi samun hakkoki irin na dakarun tsaron kasar da kuma wasu dokoki da suka shafi yin hidima kamar yadda ake yi dakarun tsaron kasar.

Cikin wannan kudiri, daga yanzu za a fara karbar dakarun sa kai din a jami'o'in horar da sojojin kasar ta Iraki.

A shekarar 2016 da ta gabata ce, majalisar dokokin kasar ta Iraki ta amince da cewa dakarun sa kai na kasar wani bangare na Dakarun tsaron kasar.