Sojojin Syria Sun Kwato Birnin Tadmor (Palmyra) Daga ISIS
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i2929-sojojin_syria_sun_kwato_birnin_tadmor_(palmyra)_daga_isis
Sojojin Syria tare da mayakn kungiyar Hizbullah sun kwace iko da birnin tarihi na Tadmor (Palmyra) daga hannun 'yan ta'addan takfiriyyah na Daesh (ISIS) da ke samun goyon bayan wasu kasashen larabawa.
(last modified 2018-08-22T06:58:02+00:00 )
Mar 25, 2016 11:48 UTC
  • Sojojin Syria Sun Kwato Birnin  Tadmor (Palmyra) Daga ISIS

Sojojin Syria tare da mayakn kungiyar Hizbullah sun kwace iko da birnin tarihi na Tadmor (Palmyra) daga hannun 'yan ta'addan takfiriyyah na Daesh (ISIS) da ke samun goyon bayan wasu kasashen larabawa.

Tashar talabijin ta Al-Ikhbariyyah ta kasar Syria ta bayar da rahoton cewa, sojojin kasar ta Syria tare da mayakan Hizbullah sun shiga cikin garin Tadmor (pamyra) a yau Juma'a, kuma sun fatattaki 'yan ta'addan Daesh, bayan halaka adadi mai yawa daga cikinsu.

Birnin Tadmor dai yana daya daga cikin birane na tarihi da suka fi dadewa a duniya, wanda hukumar UNESCO ta sanya shi daga cikin biranan tarihi na duniya, wanda 'yan ta'addan Daesh tare da taimakon masu daukar nauyinsu suka kace iko da shi, inda suka rusa wasu daga cikin kayan tarihi da ke wurin na tsawon dubban shekaru.