Sojojin Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Sun Jikkata Falasdinawa Masu Yawa
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun farma Falasdinawa da suke gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin amincewarsu da duk wani kokarin maida birnin Qudus fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila.
A zanga- zangar da al'ummar Falasdinu suka fito a jiya Juma'a domin jaddada matsayinsu na rashin amincewa da duk wani kokarin maida birnin Qudus fadar mulkin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila sun fuskanci harin wuce gona da iri daga sojojin gwamnatin Yahudawan Sahayoniyya da ya yi sanadiyyar jikkatan Falasdinawa akalla goma.
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar ta Isra'ila sun harba iskar gas mai guba kan masu zanga-zangar lamarin da ya wurga da dama daga cikin masu gudanar da zanga-zangar cikin mummunar yana yi, kuma halin goma daga cikinsu ya tsananta.
Har ila yau a farmakin da sojojin haramtacciyar kasar ta Isra'ila suka kai kan yankin garin Ramallah sun yi dauki ba dadi da matasan Falasdinawa, inda suka jikkata Falasdinawa akalla hudu ta hanyar harbi da bindiga.
Tun a ranar 6 ga watan Disamban shekara ta 2017 ce shugaban kasar Amurka Donald Trump ya shelanta birnin Qudus mallakin Falasdinawa a matsayin fadar mulkin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila lamarin da ya fuskanci maida martani daga kasashen duniya ciki har da kawayen Amurka na yammacin Turai. Sannan bayan maida lamarin zuwa babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a ranar 21 ga watan na Disamba kasashen duniya 128 suka kada kuri'ar goyon bayan Qudus a matsayin mallakin Falasdinu, yayin da kasashen 9 suka goyi bayan shirin Trump, sannan wasu kasashe 35 suka ki bayyana ra'ayinsu.