Sojojin Isra'ila Sun Jikkata Wani Bapalastine Da Harshahi
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i29738-sojojin_isra'ila_sun_jikkata_wani_bapalastine_da_harshahi
Dakarun tsaron Haramtacciyar kasar Isra'ila sun harbi wani Bapalastine a gabashin Baitul-Makdis, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatarsa
(last modified 2018-08-22T07:01:40+00:00 )
Apr 08, 2018 14:32 UTC
  • Sojojin Isra'ila Sun Jikkata Wani Bapalastine Da Harshahi

Dakarun tsaron Haramtacciyar kasar Isra'ila sun harbi wani Bapalastine a gabashin Baitul-Makdis, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatarsa

Cibiyar sadarwar Palastinu ta sanar da cewa a wannan lahadi Sojojin Isra'ila sun jikkata wani matashin Bapalastine a kusa da kauyen Ma'ale Adumim na yahudawa dake gabashin Baitul-makdis ta hanyar harbisa da bindiga.

Yahudawan  sun yi da'awar cewa matashin Bapalastinan na kokarin kai hari ne kan jami'an tsaron Isra'ilan da wuka.

A bangare guda, Wasu Yahudawa 33 karkshin tsaron jami'an tsaron Isra'ila sun kai farmaki masallacin Aksa ta hanyar kofar Babul Magaribat,sannan kuma sojojin na Isra'ila sun mayar da masallacin Aksar wani sansanin Soja.

Har ila yau, a bangare guda, Palastinawa  na ci gaba da zanga-zangar neman 'yanci a a yankin Zirin Gaza, su kuma sojojin Isra'ila na ci gaba da kame su, inda a wannan lahadi suka kame wata mata da 'ya'yanta.