Yemen: Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kashe Fararen Hula 17 A Ta'iz
Tashar talabijin din al-Masirah ta ba da labarin cewa jiragen yakin Saudiyyar sun kai hari ne akan gidajen mutane a yankin Damna Khadir da ke a gundumar Ta'iz.
Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su da akwai mutane 12 daga cikin iyali guda da su ka hada kananan yara da mata.
A wani harin da jiragen su ka kai a yankin al-mahul a cikin gundumar ta Ta'iz wasu mutum guda ya rasa ransa yayin da wasu hudu su ka jikkata.
A ranar asabar din da ta gabata ma dai jiragen yakin Saudiyyar sun kai hari a gundumar Hudaidah da ke yammacin kasar,inda su ka kashe wani fitaccen dan wasan kwallon kafar kasar, mai suna Abduljabbar Idrisi.
A watan Maris na 2015 ne dai Saudiyya da kawayenta su ka shelanta yaki akan kasar Yemen da al'ummarta wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci rayukan dubban mutane.