Ban-Ki-Moon Ya Bukaci 'Yan Siyasa Iraki Dasu Hada Kai
-
Mr Ban ki-moon da firaministan Iraki Haidar Al'Abadi
Babban sakatare na MDD Ban ki Moon ya bukaci 'yan siyasa a kasar Iraki dasu taimakawa firaministan kasar Haidar Al-Abadi domin hada kan al'ummar kasar.
Mr Ban ya bayana hakan a zauren 'yan majalisar dokokin kasar a yayin ziyara daya soma yau Asabar a Bagadaza, inda yayi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki na kasar dasu hada kai domin cimma gurin hada kan al'umma wannan kasar dake fuskantar kalubaloli da dama da suka hada da barazana ta'adanci.
Ana dai bukatar bangaran zartaswa da na dokoki a wannan kasa dasu yi aiki tare domin ciyar da gaba tare da kama ma firaministan kasar wajen shawo kan matsalolin da suka addabi wannan kasa.
A halin yanzu kasar Iraki na fama ne da faduwar farashin man fetur wanda ya kasance daya daga cikin hanyoyin samar da kudin shiga ga wannan kasa, sai kuma uwa uba makuden kudaden da kasar ke kashewa wajen yaki 'yan ta'adan (IS).