Dakarun Sama Na Kasar Yemen Sun Kai Hari Saudiya
Dakarun saman kasar yemen sun kai hari da makamai masu Linzami a filin sauka da tashi na jiragen Abha na da kuma cibiyar Man fetir na Aramko dake kasar Saudiya.
Tashar Talabijin din Al-masira ta kasar Yemen ta habarta cewa bayan harin da dakarun sojan saman suka kai da makami mai lanzami samfarin Kasif na daya a filin sauka da tashi na Abha a Asir, an dakatar da duk wani tashi da sauka na jiragen sama a filin jirgin.
Har ila yau dakarun sojan saman na yemen sun kai hari da irin wannan makami mai Linzami na Kasif na daya kan cibiyar man fetir ta Aramko dake jahar Jizan dake kudancin Saudiya.
Tun bayan da sojojin yemen din suka kera wannan nau'i na makami mai Linzami shekaru biyu da suka gabata, Dakarun Ansarullah suka dauki alkawarin inganta wannan makami, inda a halin da ake ciki ya kan iya daukan kilo 30 na ababen fashewa.