Gaza: Palasdinawa 30 Sun Jikkata daga harin Sojojin Sahayoniya
Juma'a ta uku kenan da al'ummar palasdinu take gudanar da Zanga-zangar hakkin komawa gida akan iyakar Gaza da palasdinu da ke karkashin mamaya
A yayin Zanga-zangar ta yau, palasdinawan sun kona tayoyi domin kange kawunansu daga harbin sojojin sahayoniya, kamar kuma yadda su ka kona tutocin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Har ila yau, palasdinawan sun rika ba da taken; Hakkin alummar Palasdinu na komawa zuwa gidajensu na gado da 'yan sahayoniya su ka kwace a yayin kafa haramtacciyar kasar Isra'ila.
Juma'a ta uku kenan a jere da palasdinawa su ke fitowa domin yin Zanga-zanga. Makwanni uku da suka gabata 'yan sahayoniyar sun kashe palasdinawa 18 a rana guda, yayin da suka jikka wasu fiye da 100.
Amurka ta hau kujerar naki a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya domin hana a yi tir da kisan palasdinawa da 'yan sahayoniya su ka yi.