Yemen: An Kashe 'Yan Koran Saudiyya 34
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i29926-yemen_an_kashe_'yan_koran_saudiyya_34
Majiyar sojan Yemen ce ta sanar da kashe 'yan koran Saudiyyar 34 a yankin Ta'iz da Jaufa a al-baidha'a.
(last modified 2018-08-22T07:01:42+00:00 )
Apr 15, 2018 06:38 UTC
  • Yemen: An Kashe 'Yan Koran Saudiyya 34

Majiyar sojan Yemen ce ta sanar da kashe 'yan koran Saudiyyar 34 a yankin Ta'iz da Jaufa a al-baidha'a.

Tashar talabijin din al-Masirah ta Yemen ta ba da labarin cewa wani kwararren maharbi na sojan kasar ne kashe 'yan koren Saudiyyar da ke karkashin gwamnatin Abdulhadi Mansur mai murabus.

A wani gefen manyan bindigogin sojojin Yemen sun kai farmaki a sansanonin sojan Saudiyya da suke a Najran, tare da hallaka soja guda a yankin al-shbakah.

Sojojin Saudiyya bisa taimakon Amurka da turai suna ci gaba da kai hare-hare a bangarori daban-daban na kasar Yemen, tun daga shekarar 2015. Kawo ya zuwa yanzu adadin mutanen da su ka mutu sanadiyyar yakin sun haura 15,000.