Sojojin Syria Sun Kammala Tsarkake Yankin Qalamun Daga 'Yan Ta'adda
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i30298-sojojin_syria_sun_kammala_tsarkake_yankin_qalamun_daga_'yan_ta'adda
Rundunar sojin kasar Syria ta sanar da kammala tsarake yankin Qalamun baki daya daga dukkanin 'yan ta'addan wtakfiriyya ta suka kafa tunga a wurin.
(last modified 2018-08-22T07:01:45+00:00 )
Apr 26, 2018 02:12 UTC
  • Sojojin Syria Sun Kammala Tsarkake Yankin Qalamun Daga 'Yan Ta'adda

Rundunar sojin kasar Syria ta sanar da kammala tsarake yankin Qalamun baki daya daga dukkanin 'yan ta'addan wtakfiriyya ta suka kafa tunga a wurin.

Kamfanin dillancin labaran SANA ya bayar da rahoton cewa, bayan kammala tsarkake yankin Ghouta baki daya daga 'yan ta'adda na kasashen duniya da suka mayar da wurin wata tungarsu, a jiya Laraba kuma an tsarkake yanin Qalamun wanda shi ma daya ne daga cikin yankunan da 'yan ta'addan suka kafa sansanoni.

Bayan halaka wani adadi daga cikin 'yan ta'addan wadanda suke da alaka da kungiyoyin wahabiyawa daban-daban daga kasashen duniya, daga karshe sun a ince su fice daga yankin bayan sun ajiye makamansu, kuma za su nufi yankunan da ke kan iyaka da kasar Turkiya, wadanda akasari da ma ta nan ne suka shigo cikin kasar ta Syria.