Jiragen Yakin Kawancen Saudiya Sun Kai Hari Yankin Sa'ada Na Yemen
Jiragen yakin kawancen Saudiya sun yi lugudar wuta kan yankin Raazih na jahar Sa'ada dake arewacin yemen
Kamfanin dillancin labaran Almasira na kasar yemen ya nakalto shaidu daga yankin na cewa jiragen yakin kawancen saudiya sun kai hari har so biyu a yankin ba tare da karin haske ba kan hasarar da hare-haren suka janyo ba.
A jiya Talata ma jiragen yakin kawancen saudiyar sun kadamar da hare-hare har so 20 a yankuna daban-daban na jahar ta Sa'ada.
A matsayin mayar da martani Sojojin kasar Yemen da dakarun sa kai na kasar na ci gaba da kai hare-hare cikin kasar ta Saudiya, inda ko a jiya ma kafafen yada labaran Saudiyar suka tabbatar da hallakar Sojojin kasar 4 a yankunan kai iyakar kasar da Yemen sanadiyar farmkin da Dakarun kasar ta Yemen suka kai musu.
Tun a 2015 ne dai sojojin na kasar Saudiyya suka fara kai hari akan kasar Yemen tare da cikakken goyon bayan Amurka, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci fiye da rayuka 12,000 bisa kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.