Nasarar Kungiyar Hizbullah Da Kawayenta A Zaben 'Yan Majaisa.
Rahotanni daga kasar Labanon na nuni da cewa kungiyoyin Hibzullah da Amal da kawayensu sun sami gagarumar nasara a zaben 'yan majalisar kasar da aka gudanar ranar Lahadi da ta gabata, yayin da jam'iyar Mustakbal da Sa'ad Hariri ke jagoranta ta sha kashi, duk kuwa da irin makudan kudaden da suka kashe a yakin neman zabe.
Bayan shekaru 5 na jinkiri, a ranar lahadin da ta gabata ce aka gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar Labnon, inda 'yan takara 583 a mazabu 15 na kasar suka fafata da juna, a cewar Nehad Al-Mashnuk ministan cikin gidan kasar sama da kashi 49% na mutanan da suka caccanci kada kuri'a ne suka gudanar da zaben na ranar lahadi.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa sakamakon zaben 'yan Majalisar na kasar ta Labnon na nuni da cewa kungiyoyin Hibzullah da Amal da kawayensu sun sami gagarumar nasara a zaben 'yan majalisar kasar,inda suka samu kujeru sama da yadda suka yi hasashe kafin gudanar da zaben.
A tasa bangare Jam'iyar Mustakbal ta Sa'ad hariri ya rasa kashi daya cikin uku na yawan kujerun da take da shi a majalisar dokokin kasar, sakamakon karshe da aka bayyana a wasu mazabun da jam'iyar ke da karfi a Bairout da Trablus, an bayyana cewa jam'iyar ta kwashi kashinta a hanu, daga hadakar 'yan takara na Fata da cika alakawri na kungiyoyin Hizbullah da Amal da kawayensu.baya ga wannan nasarar,ga wasu sabin fuskoki a bangaren siyasa masu adawa da manufofin jam'iyar Almustakbal kamar Major Janar Jamil Sayyid wanda aka daure shi kan zarkin kisan Rafik Hariri ma'aifin Sa'ad hariri na daga cikin ababen dake bayyana cewa al'ummar kasar Labnon sun fara dawo daga rakiyar manufofin jam'iyar Mustakbal.
Sakamakon zaben 'yan Majalisar na Labnon ya bayar da muhimin sako kamar haka: nasarar gwagwarmaya da faduwar manufofin saudiya da kasashen yamma gami da Amurka a kasar Labnon, kuma shakka babu wannan sakamako zai taka muhimiyar rawa ga matsayin gwagwarmaya wajen tabbatar da tsaron kasar Labnon da kuma ci gaba da yakar 'yan ta'adda a kasar Siriya, kuma wannan shi ke nuna cewa mafi yawa daga cikin al'ummar kasar Labnon sun gamsu da rawar da kungiyar Hizbullah ke takawa wajen kare kasar daga mamayar Haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma yaki da ta'addanci a kan iyakar kasar da Siriya.sannan kuma hakan ya nuna cewa al'ummar kasar sun kosa da siyarar hukumomin birnin Riyad a harakokin cikin gidan kasar, abinda ya wakana a watan Nuwambar 2017, inda yarima mai jiran gado na saudiya Muhamad bn Salman ya kira Piraministan kasar Labnon Sa'ad Hariri sannan ya bukaci ya karanta wata takarda da suka rubuta masa na yin murabus, wannan lamari dai na daga cikin abinda masana ke ganinsa a matsayin dalinin rashin cin nasarar Hariri a zaben 'yan Majalisar da ya gabata.
Yayin da yake sharhi kan zaben kasar ta Labnon Muhamad Ali Muhtadi masanin harakokin siyasar kasshen Larabawa ya ce sakamakon zaben 'yan majalisar kasar Labnon ya nuna sha kashin Saudiya a kasar karara, kuma duk da irin makudan kudin da kasashen Saudiya da hadaddiyar daular labarawa suka kashe a yayin yakin neman zabe da kuma irin wa'adi da kalaman Amurka tare da barazanar hukumomin Isra'ila, hakan ya kasa nisantar da al'ummar Labnon daga kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah, wannan shan kashi da 'yan koran kasashen yamman suka sha a Labnon har ta kai ga Asharaf Raifi, Shugaban jami'an 'yan sandar kasar kuma tsohon ministan shari'a da ya yi kaurin suna wajen sukan kungiyar Hizbullah da kasar Saudiya ta yi masa alkawarin kujerar Piraministan kasar bayan magoya bayanta sun ci zabe, kasa samun kuru'u na shiga Majalisar dokokin kasar.
Abin tuni a nan dai shi ne duk da irin rinjayen da kungiyar Hizbullah da Amal tare da kawayensu suka samu a majalisar dokokin kasar, to amma ana zabar Piraministan kasar ne daga bangaren Ahlusunna bisa yarjejjeniyar da al'ummar kasar suka cimma kamar yadda kujerar Shugaban Majalisar dokoki ke fitowa daga bangaren 'yan shi'a, shi kuma Shugaban kasa daga bangaren mabiya addinin Kirista.