Syria: Mutane Biyu Sun Mutu A Wani Harin Sojojin Sahayoniya
Majiyar tsaron kasar Syria ta ce a jiya da dare ne jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila su ka kai hari a kusa da birnin Damascuss wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula biyu
Kamfanin dillancin labarun Syria na "Sana" ya ambato majiyar asibiti tana tabbatar da kai harin jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila a yankin al-kasurah' da ke kudu da birnin Damascuss, wanda ya ci rayyukan fararen hula biyu.
Tashar talabijin Akhbariyyah, ta syria ta ce; An kakkabo dukkanin makamai masu linzamin da jiragen yakin su ka harba. Bugu da kari tashar ta nuna hotunan wurin da aka kai wa harin da baraguzan makamai masu linzamin da aka harbo.
Bayan da sojojin Syria da kawayensu su ka murkushe kungiyoyin 'yan ta'adda, haramtacciyar Kasar Isra'ila ta bude kai wa Syria hari daga lokaci zuwa lokaci.