Yemen: An Halaka 'Yan Koren Saudiyya A Gundumar Ta'iz
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i30660-yemen_an_halaka_'yan_koren_saudiyya_a_gundumar_ta'iz
Sojojin Yemen sun kai harin da su ka shammati 'yan koren Saudiyya da ke gundumar Ta'iz a yankin Kudu maso yammacin kasar ta Yemen
(last modified 2018-08-22T07:01:48+00:00 )
May 09, 2018 02:26 UTC
  • Yemen: An Halaka 'Yan Koren Saudiyya A Gundumar Ta'iz

Sojojin Yemen sun kai harin da su ka shammati 'yan koren Saudiyya da ke gundumar Ta'iz a yankin Kudu maso yammacin kasar ta Yemen

Kafafenn watsa labarun Yemen sun ambaci cewa a yayin harin an kashe 'yan koren Saudiyya da dama da kuma jikkata wasu.

Wata majiyar sojan Yemen ta ce; mayaka 9 masu alaka da Abdu Rabbuh Mansur Hadi ne aka kashe a wani harin da aka kai musu a gundumar Sa'adha da ke arewacin kasar.

A lokaci guda kuma jiragen yakin Saudiyya sun kai wasu hare-haren a gundumar Ma'arib.

Saudiyya bisa cikakken goyon baya da kuma taimakon Amurka sun bude kai wa Yemen hari tun 2015, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci rayukan mutane 13,000.