Sojojin Isra'ila Sun Kai Farmaki A Yankin Zirin Gaza
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i31020-sojojin_isra'ila_sun_kai_farmaki_a_yankin_zirin_gaza
Sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai hare-hare kan wuraren kungiyar gwagwarmayar Palastinawa a gabashin sansanin Albarij na Zirin Gaza a wannan Talata
(last modified 2018-08-22T07:01:52+00:00 )
May 22, 2018 06:34 UTC
  • Sojojin Isra'ila Sun Kai Farmaki A Yankin Zirin Gaza

Sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai hare-hare kan wuraren kungiyar gwagwarmayar Palastinawa a gabashin sansanin Albarij na Zirin Gaza a wannan Talata

Cibiyar yada labaran Palastinu ta habarta cewa dakarun tsaron Isra'ila sun kai farmaki har ila yau a yankuna da dama na kusa na sansanin Al-Auda na gabashin Albarij. inda suka yi da'awar cewa sun kai harin ne a yayin da wasu matasan Palastinawa suke yin yunkurin shiga cikin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Har ila yau a jijjifin safiyar yau Talata, sojojin Isra'ilan sun kai hari a buranan Qudus, Alkhalil da Ramulla dake gabar tekun Jodan tare kuma da yin awan gaba da wasu matasan Palastinawa 11.

A ko wata rana Sojojin Isra'ila na kai farmaki gidajen Palastinawa a yankin gabar tekun Jodan da Qudus, alkaluma sun nuna cewa akwai palastinawa 6500  cikinsu hardakananen yara kimanin 300 a gidajen yarin Isra'ila.